Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane Sama Da Ashirin A Jihar Adamawa


Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadiyar Mutuwar Mutane Sama Da Ashirin Da Jikkata Wasu A Jihar Adamawa
Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadiyar Mutuwar Mutane Sama Da Ashirin Da Jikkata Wasu A Jihar Adamawa

Ambaliyar ruwa ta sanadin mutuwar mutane sama da ashirin da biyar da kuma jikkata fiye da hamsin, al’amarin da ya janyo rushewar ginin wani makaratar yara na  jeka ka dawo a karamar hukumar Yola ta kudu a Jihar Adamawa.

ADAMAWA, NIGERIA - Dr. Muhammad Aminu Sulaimani sakataren hukumar bada agajin gaggawa na Jihar Adamawa ne ya tabbatar mana da aukuwar ambaliyar da ta yi sanadin rasuwar mutanen a Jihar.

Aliyu Sarkin Matasa, mahaifin wani dalibin da lamarin rushewar ginin ya yi sanadin karyewar hanunsa, ya ce wannan ambaliyar ruwa, Allah ne ya kawo ta, saboda haka sun dauki kaddara, yaransu kuma Allah ya kawo masu sauki.

Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadiyar Mutuwar Mutane Sama Da Ashirin Da Jikkata Wasu A Jihar Adamawa
Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadiyar Mutuwar Mutane Sama Da Ashirin Da Jikkata Wasu A Jihar Adamawa

Gawan Aliyu Jambutu, mahaifin wata daliba Halima Aliyu Jambutu, ya ce yanzu haka dai hannun ‘yarsa ya na karye kuma hannun ya na matukar ciwo amma suna rokon Allah ya sa haka shi ya fi alheri a gare su baki daya.

Su ma malaman makarantar yaran da lamarin ya shafa, a ta bakin malama Hafsat Dallahtu ta ce sun yi matukar shiga cikin tashin hankali da faruwar ambaliyar.

Saurari rahoto na musamman daga Lado Salisu Muhammad Garba:

Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadiyar Mutuwar Mutane Sama Da Ashirin A Jihar Adamawa.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG