Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Wadanda Ambaliyar Ruwa Ya Halaka a Najeriya Ya Haura 600 -Gwamnati


An gano wasu motoci a nutse a cikin ruwa a wani gidan mai dake Lokoja, Nigeria 13 ga Oktoba, 2022.
An gano wasu motoci a nutse a cikin ruwa a wani gidan mai dake Lokoja, Nigeria 13 ga Oktoba, 2022.

A yanzu haka sama da mutane 600 ne aka tabbatar sun mutu a ambaliyar ruwa mafi muni cikin shekaru goma a Najeriya, a cewar wani sabon adadin da aka fitar jiya Lahadi.

Bala'in ya kuma tilastawa sama da mutane miliyan 1.3 barin gidajensu, in ji wata sanarwa da ma'aikatar jinkai ta Najeriya ta fitar a shafinta na Twitter.

“Abin takaici, an rasa rayuka sama da 603 ya zuwa yau 16 ga Oktoba, 2022,” in ji ministar harkokin jin kai Sadiya Umar Farouq.

Barnar Ambaliyar ruwa
Barnar Ambaliyar ruwa

Adadin wadanda suka rasu na makon da ya gabata sun kai 500, amma adadin ya karu a wani bangare saboda wasu gwamnatocin jihohi ba su shiri tunkarar ambaliyar ba, in ji Ministan.

Ambaliyar ta kuma lalata gidaje sama da 82,000 da kuma gonaki kusan hekta 110,000 (kadada 272,000) inji Umar Farouq.

AMBALIYA
AMBALIYA

Yayin da damina ta kan fara ne a cikin watan Yuni, ruwan sama ya yi yawa musamman tun watan Agusta, a cewar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA).

A shekarar 2012, mutane 363 ne suka mutu yayin da sama da miliyan 2.1 suka rasa muhallansu sakamakon ambaliyar ruwa.

Mutane Fiye Da 200 Su Rasa Muhalin Su A Karamar Hukumar Maru A Jihar Zamfara.
Mutane Fiye Da 200 Su Rasa Muhalin Su A Karamar Hukumar Maru A Jihar Zamfara.

Kasashen Afirka da ke kudu da hamadar sahara na fama da matsalar sauyin yanayi kuma yawancin tattalin arzikinsu na cigaba da kokawa da illar yakin Rasha da Ukraine.

Masu noman shinkafa sun yi gargadin cewa mummunar ambaliyar ruwa na iya yin tasiri a farashin kasar na kimanin mutane miliyan 200 inda aka hana shigo da shinkafa don tada noman cikin gida.

Hukumar samar da abinci ta duniya da hukumar abinci da noma ta Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana cewa a watan da ya gabata Najeriya na cikin kasashe shida da ke fuskantar barazanar bala'in yunwa.

~AP

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG