Matsalar Faduwar Manyan Motoci Na Ci Wa Jama'ar Garin Goure Tuwo A Kwarya

Faduwar wata babbar Mota a Afirka Ta Kudu

Gwamnatin Nijar ta bayyana shirin aika da kwararu domin su gudanar da bincike a garin Goure da ke yankin Zinder bayan da jama’ar garin suka koka kan yadda ta'azzarar faduwar tireloli da motocin dakon man fetur a kan babbar hanyar garin ke barazana ga rayuwarsu.

Al'ummar Goure sun isar da kokensu ga dan majalisa Honorable Liman Amadou mai wakiltar mazabar Goure. Lamarin da ya yi sanadin mutuwar jama'ar da ba su ji ba su gani ba, ciki har da yara.

Duk da cewa Gundumar Goure ta kasance daya daga cikin wuraren farko da aka kafa tsarin fasalta yankunan karkara jim kadan da samun 'yancin Jamhuriyar Nijar, har yanzu hanya daya ce tak ke ratsa garin wadda ke fita daga Zinder zuwa Diffa. A saboda haka ne wannan matsalar ke kawo babbar cikas ga harkokin yau da kullum.

"Idan mota ya fadi, hanyar tana rufewa har na kwanaki biyu, babu motar da ke wucewa," inji Honorable Liman.

Ministan ayyukan gine-gine da tattalin hanyoyin zirga-zirgar kasa, Kadi Abdullahi, ya bada tabbacin za su aika da kwararru da zasu gudanar da bincike domin samo bakin zaren wannan matsalar.

Saurari cikakken rohoton Sule Mumini Barma

Your browser doesn’t support HTML5

Yawaitar Faduwar Motoci a Goure - 2' 39"