Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ruwan Sama Kamar Da Bakin Kwarya Ya Hallaka Mutane Da Dama a Kasashen Gabashin Afirka


Ismael Omar Guelleh, shugaban kasar Djibouti daya daga cikin kasar da ruwan ya shafa a gabashin Afirka
Ismael Omar Guelleh, shugaban kasar Djibouti daya daga cikin kasar da ruwan ya shafa a gabashin Afirka

Sama da mutane 22 suka mutu sanadiyar ruwan sama kamar da bakin kwarya da iska kana wasu da dama suka bata a kasashen gabashin Afirka da suka hada da Somalia, Ehiopia, Eritrea da Djibouti

A kalla mutane 22 ne suka mutu yayin da wasu kuma suka bata sakamakon wani ruwan sama kamar da bakin kwarya da yazo da iska mai karfin gaske a yankin kasashen gabashin Afrca da suka hada Ethiopia,Somalia,Eretrea, da Djibouti.

A kalla mutane 15 ne suka mutu a gundumar Awdal, yankin dake cikin jamhuriyar Somali, kamar yadda gwamnan yankin Abdirahaman Ahmed Ali yake cewa, haka kuma wani, mutum guda ya rasu a garin Berbera dake gundumar Sahil.

Sai dai gwamna Ali yace wannan adadin na wucin gadi ne domin ko adaddin na iya karuwa domin ko ana nan ana kokarin ganin an shiga cikin kauyukan da wannan bala’in ya auka mawa.

Ana kyautata zaton yawancin wadanda wannan lamarin ya rutsa dasu ruwan ne ya wuce dasu kamar yadda mazauna wannan wurin ke cewa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG