A yammacin garin Agadez dake da tazarar kilomita 25 da hedkwatar jihar ta Agadez jami’an tsaro da suka kai wani samame suka yi wawan kamun makamai da dama da tulin harsashai kamar yadda suka bayyana wa manema labarai.
Hukumomin jihar ta Agadez ta bakin magatakardan gwamnan jihar Malam Attahiru Adam suka jinjinawa jami’an tsaron kasar a madadin gwamnan jihar da hukumomin kolin Jamhuriyar Nijar gaba daya dangane da jan aikin da suka yi.
A cewar Malam Attahiru Adam ba abun murna ba ne ganin irin muggan makaman cikin kasarsu sai dai suna jinjinawa jami’an tsaro bisa ga kokarin da suka yi na gano rumbun makaman. Ya godewa talakawa ma da suka bada hadin kai aka cimma nasarar. Ya yi kira ga talakawa su kwantar da hankalinsu tareda fatan Allah ya tona asirin duk wani dake da wani mugun hufi.
Kawo yanzu dai hukumomi sun damke mutane biyar da ake zargin suna da alaka da makaman da kuma boyesu.
Daya daga cikin wakilan kwamitin samun zaman lafiya na jihar Butadi Cuweran ya yi kira ga gwamnati data samar ma matasan yankin aiki. Rashin samar ma matasan jihar aiki ke haddasasu yin fataucin makamai saboda ko a ranar 7 ga wannan watan jami’an tsaro sun cafke wasu makamai manya da kanana a cikin jihar da aka boye cikin akwatunan talibijan da naurorin kwamfuta.
Ga rahoton Haruna da karin bayani
Facebook Forum