Wannan dai na zuwa ne yayin da ma’aikatan jinya a kasar ke cikin wani yajin aikin da suka shafe fiye da makwanni biyu suna yi.
Kwararrun na asibitin gwamnatin tarayyar da ake cewa FMC, Yola ne tare da tawagar wasu da aka gayyato ne suka gudanar da wannan aikin fida na raba tagwaye mata da aka haifa a manne da juna. An yi aikin fidan cikin nasara.
Farfesa Muhammad Auwal shugaban asibitin, wanda kuma shi ya jagoranci wannan aikin fidan,yace samun nasarar fidar,abun farin ciki ne.
Haka nan kuma Farfesa Auwal ya bukaci jama’a da kan haifi irin wadannan jarirai a manne, da kada ayi kasa a gwiwa wajen kawo su asibiti domin dubawa.
Malama Killo Adam, itace mahaifiyar mannanun yaran biyu ta ce tabarkallah! Haka nan kuma tayi kira ga hukumomin Najeriya sun taimaka ganin cewa wasu lokutan sai an hada da kasashen waje domin irin wannan aiki.
Hukumar gudanarwar asibitin ne dai ta daukin nauyin gudanar da aikin kyauta.
Ga raoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani
Facebook Forum