Masu Fafutuka Sun Zargi Tsohon Shugaba Mahamadou Issouhou Da Hannu A Juyin Mulkin Nijar

Shugaba Issouhou Mahamadou

Sai dai makusantan tsohon shugaban sun musanta wannan zargi, suna masu cewa har da dansa aka tsare a juyin mulkin da aka yi.

NIAMEY, NIGER. - Kungiyoyin dai sun yi kira ga sojojin juyin mulkin da su cafke Shugaba Issouhou saboda laifukan da suke zargin ya tafka a zamanin mulkinsa na tsawon shekaru goma. Sai dai wasu makusantansa na kallon wadannan zarge-zarge a matsayin marassa tushe.

La’akari da wasu tarin bayanan da suka ce sun tattara daga ranar faruwar juyin mulkin kawo wannan lokaci ya sa wasu kungiyoyin fafutikar Nijar zargin tsohon Shugaban kasa Issouhou Mahamadou a sahun wadanda ke da alhakin kifar da Shugaba Mohamed Bazoum a cewar shugaban kungiyar Tounons La page Maikol Zodi.

Wasu bayanan na daban na kara karfafa wa ‘yan kasar Nijar kwarin guiwa a zargin da suke yi wa Shugaba Issouhou da yin buris da abubuwan da ke faruwa a wannan kasa.

Tournons la Page ta ce ta samu wasu bayanan da ke nunin Shugaba Issouhou na da niyyar zuwa Abuja don ganawa da Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, mafari kenan shugabaninta suka kudiri aniyar hana wannan tafiya.

A wani labarin da ke da nasaba da yanayin siyasar Nijar majalissar sojoji ta CNSP ta umurci jakadan kasar dake Cote d’ivoire da ya dawo gida sakamakon kalaman da Shugaba Alassan Ouattara ya furta a washe garin taron kungiyar CEDEAO da ke jaddada aniyar amfani da karfin soja don mayar da Mohamed Bazoum kan mukaminsa.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Masu Fafutika Sun Zargi Tsohon Shugaba Issouhou Mahamadou da Hannu A Juyin Mulkin.mp3