A wannan fafatawa tsakanin shugaba Donald Trump da ke neman wa’adin mulki na 2, da tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden, wani abu ne da masu sharhi akan al’amuran yau da kullum ke bayyana ra’ayoyi mabambanta a kai.
Wani dan rajin kare dimokradiyya shugaban kungiyar Voix des sans Voix Nassirou Saidou, na ganin alamun wannan zabe zai samar da sauyin da zai bai wa dan takarar Democrat Joe Biden damar doke abokin karawarsa.
To sai dai a nasa gefe mai sharhi akan al’amuran yau da kullum Abdourahamane Alkassoum, na cewa har yanzu dan takarar jam’iyyar Republican na da farin jinin da zai bashi damar sake samun wani sabon wa’adin mulki.
Kasar Amurka ta yi fice a duniya akan maganar tsare-tsaren zabe inda komai ke gudana ba tare da faruwar irin hatsaniyar da aka saba gani a wasu kasashen Afrika ba, gabanin zabe ko a ranar zabe da ma zuwa lokacin bayyana sakamako, wani abu da ya zama wajibi ‘yan siyasar Nijer su bude ido don koyon darussa daga zaben.
Yanzu dai hankula sun karkata wajen kasar ta Amurka, domin jin yadda za ta kaya a wannan zabe da ya zo da sauye-sauye a wannan karon, saboda annobar coronavirus da ake fama da ita, bayanai sun nuna cewa tuni miliyon Amurkawa suka kada kuri’un su ta hanyar gidan waya, don kaucewa shiga layin masu zabe a ranar Talata 3 ga watan Nuwamba.
Your browser doesn’t support HTML5