Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Amurka Ya Dauke Hankalin 'Yan Najeriya


Donald Trump da Joe Biden
Donald Trump da Joe Biden

A yayin da Amurkawa ke kakkabe shimfidar shiga fagen kada kuri'a zaben shugaban kasa, Wasu masu fashin baki kan harkokin yau da kullun a Najeriya na cigaba da yin tsokaci a kan zaben na Amurka.

Wasu masu fashin baki dai na ganin Zaben shugaban kasar Amurka na wannan mako ya jawo hankali 'yan Afirika da dama saboda wasu manyan dalilai. Lawya mai zaman kanshi a Kaduna, Barr. El-zubair Abubakar na cikin masu nazari gameda Zaben na Amurka.

Ya ce zaben Amurka yafi maida hankali a kan batun yaki da murkushe ayyuakn ‘yan ta’adda musamman tun lokacin da shugaba Bush ya karbin mulkin kasar daga hannun Ragan. Amma a yanzu zaben ya karkata ne a kan abubuwa dake faruwa a gida.

Yanayin gudanar da zaben America da kuma lamurran da kan biyo bayan Zaben na cikin abubuwan da ke jawo hankali wasu 'yan-Najeriya.

Galibin ‘yan Najeriya sun sha’awarsu a kan yanda ake gudanar da zaben Amurka har a bayyana wanda ya yi nasara ba tare da samun tashin hankali ba. Sun kuma yabawa kyakkyawar mu’amala tsakanin ‘yan takara ba kamar Najeriya ynda ake daukar abokin takara a matsayin abokin gaba.

Wasu 'yan-Najeriya dai na ganin Najeriya na da darasin da za ta dauka gameda Zaben na Amurka.

Gobe Talata 3 ga watan Nuwamban nan ne dai za a kada kuri'ar Zaben shugaban kasar Amurka tsakanin Donald Trump na jamiyyar Republican mai Mulki da kuma Joe Biden na Democrat.

Ga dai rahoton Isah Lawal Ikara daga Kaduna a Nageriya:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:38 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG