Yakin neman wannan kujerar don maye gurbin Roberto Azevedo, dan kasar Brazil, ya dau wani sabon salo tun a ranar Laraba, bayan da Amurka ta ki amincewa da 'yar takarar Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala.
Ngozi mai shekaru 66 da haihuwa, ta samu goyon bayan da yawa daga cikin mambobin kungiyar ta WTO kasashen duniya, amma a wannan mako Amurka ta goyi bayan abokiyar takarar Ngozi, Ministar cinikayya a Korea ta Kudu Yoo Myung-hee, wacce Amurka ta ce tana da dabaru da kwarewar a fannin kasuwancin duniya.
Amma duk da haka, 'yan Najeriya sun ci gaba da nuna goyon baya ga Okonjo-Iweala, wacce ta taba rike mukamin ministar kudin kasar.
A cewar wani masanin tattalin arziki Farfesa Ken Ife, duk da rashin amincewa da Amurka ta nuna akan Ngozi, hakan ba zai shafi matsayar karshe da aka cimma ba.
“Ai ba kamar zaben shugabanin bankin duniya da na bankin ba da lamuni ba ne, wanda Amurka ke da karfin fada a ji wajen zaben shugabaninsu. Amurka kanta tana da kuri’a daya ce kacal.” Shugaban Amurka Donald Trump ya yi magana amma sauran kasashen duniya sun yi gaban kansu".
Amma dai rashin samun kuri’ar Amurka na iya sa a kara tsayin kwanakin fitar da sakamakon har na tsawon makonni ko fiye da haka.
Idan har aka zabi Ngozi a matsayin Shugaba WTO, za ta zama mace ta farko kana ‘yar Nahiyar Afrika ta da za ta shugabanci wannan hukumar da ke sa ido kan harkokin kasuwanci a duniya.
'Yan Afrika da dama sun yi ammanar cewa, idan ta zama shugabar hukumar kasashen Afrika za su samu cikakken wakilici a hukumar.
Shi kuwa Eze Onyekpere, masanin tattalin arziki, ya ce, da zarar ‘yar Afrika ta shugabanci hukumar, to babu shakka Najeriya da kasashen Afrika za su fahimci harkokin kasuwancin na duniya da kuma ire-iren damar da ake samu.
"Idan dayanmu na Turin, hakan zai rika tunatar da mu Rabin da ya kamata mu rika yi akai-akai domin samun bayanan da suka dace a kuma lokacin da ya dace saboda mu ci gajiyar irin damar da ke akwai." In ji Onyekpere
Sai dai wasu masu suka na cewa, Okonjo-Iweala ba ta da kwarewar da ta dace idan aka zo wajen maganar tattauna harkar kasuwanci. Sai dai Onyekpere bai amince da wannan ra'ayi na su ba.
"Yanayin yadda mata suke shi ne, suna da son bin al'amura ta hanyar sulhu, sun san yadda za su raba gardama su samar da maslaha. Saboda haka, in a ga za a samu huldar kasuwanci cikin lumana a duk fadin duniya." Ya kara da cewa.
Shi kuwa Farfesa Ken Ife, wanda bai nuna zabinsa ba cewa ya yi duk wadda ta samu nasarar zama shugabar hukumar, tana da kalubale a gabanta, wadanda suka hada koma baya da harkar kasuwanci ta samu a sanadiyyar rikici da ke tsakanin Amurka da China.
“Su ne kasashen duniya biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya, abin da ke faruwa a tsakaninsu na sakawa juna harajin kashi 20 ko kashi 25 na janyo tarnaki. Daya daga cikin manyan korafe-korafen shugaban Amurka Kan kungiyar ta WTO shi ne, kungiyar na jan kafa wajen sasanta wannan rikici. Sun kwashe shekaru suna korafi kan yadda ake take dokokin kasuwanci sannan China ta yi biris da lamarin." In ji Farfesa Ife.
Ita dai bukatar cike gurbin shugaban wannan kungiya ta WTO ta taso ne bayan da shugabanta Azevedo ya yi murabus shekara daya kafin wa'adinsa ya kare.
A ranar 9 ga watan Nuwamba kungiyar wacce ke da hedkwata a Geneva za ta zauna don tattauna yadda za a zabi sabon shugaban hukumar.
Facebook Forum