Matsalar tsaro da Najeriya ke fama da ita musamman a ‘yan kwanakin da suka gabata da aka yi ta gudanar da zanga zangar da ta haifar da kone konen muhimman wurare a kasar, har ya kai ga warwaso da rusa rumbunan ajiye abinci a wasu jihohi na cikin abubuwan da aka tattauna a shirin da Ofishin Muryar Amurka ya gudanar.
Da wahala a manta da al'amarin da ya faru makwannin da suka gabata a Najeriyar, inda matasa daga jihohin da dama na kasar suka gudanar da zanga zangar neman kawo karshen rundunar ‘yan sanda da ke yaki da ‘yan fashi wato SARS, wanda har ya kai ga bata gari daga cikinsu suka kwace akalar zanga-zangar zuwa sace-sace da kone-kone, da kuma fasa rumbunan ajiyar abinci na gwamnati da ma na 'yan kasuwa da sunan kwasar ganima, lamarin da ya tsananta saboda matsalar rashin doka da oda a fadin kasar.
Ofishin Sashen Hausa na Muryar Amurka a Abuja ya karbi bakwanci shugabannin al’umma don duba tasirin zanga zangar ga kasar da kuma nemo mafita dangane da sake aukuwar irin wannan lamari,
Mustapha Salisu Musa yana da Muryar Amuka ya shirya. Ya ce dole ne shugabannin kasar su yi la’akari da abubuwa dake faruwa a kasar domin kaucewa irin abubuwa da suke. Ya ce a fili batun ‘yan sandan SARS ne ya janyo zanga zanga amma a hakika mutane sun bayyana basu jin dadin kamun kudayin shugabanni.
Shiko Sabo Imam Gashuwa, masani kan harkokin siyasa a kasar, ya danganta abubuwa da suka faru ne da sakaicin gwamnatin tarayyane da shugaba Muhammadu Buhari da kuma gawarsu. Ya ce yakamata shugaban ya san kasar na cikin wani mawuyacin hali kuma ya saurari al’umma.
A nasa bangaren Matamakin kwamishinan ‘yan sanda na birnin Abuja ACP Aminu Garba, wanda ya wakilci Kwamishina Bla Ciroma ya bayyana cewa ya zuwa yanzu ‘yan Najeriya sun dau darasi.
Mun kuma ji ta bakin dan majalisa dake wakiltar jihar Zamfara Hon. Shehu Ahmad Sarkin Fulani, wanda ya bayyana cewa ta irin wannan taron ne shugabanni za su san halin da alummar su ke ciki
Manyan baki a taron dai sun hada da Abdulkarim Ibrahim shugaban kamfanin EASY GIS kana daya daga cikin jagororin wata kungiya mai suna ‘WE TOGETHER’ da kuma Barista Umar mai Nasara Kogo wanda ya yi kira a kan a mutunta dokaki da ake da su a kasar.
Ga rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim daga Abuja Najeriya:
Facebook Forum