Shekaru 50 Da Kashe Martin Luther King Jr

1965 - Martin Luther King, Jr. a lokacin da yake jawabi a garin Selma, Jihar Alabama ran 12 Fabrairu, 1965. King yayi gwagwarmaya da jami'in tsaro na Selma, watau Sherrif, Jim Clark, game da batun 'yancin jefa kuri'a da rajistar bakake a zaman masu jefa kuri'a a Selma.

1956 - A ranar 23 Fabrairu 1956, Martin Luther King, Jr., tare da Rev. Ralph D. Abernathy sun mika kawunansu ga jami'in 'yan sanda Lt. D.H. Lackey a Montgomery, Jihar Alabama, bayan da aka tuhume su da haddasa yamutsi dangane da gangamin kauracewa shiga bas-bas na birnin.

1956 - Mai dakin Martin Luther King, Jr., Coretta, tana masa marhabin bayan da ya fito kotu a birnin Montgomery ta Jihar Alabama ranar 22 Maris, 1956. Kotu ta same shi da laifin shirya gangamin kauracewa shiga bas-bas na birnin a saboda yadda ake ce bakaken fata sai a baya zasu zauna, turawa kuma a gaba.

1962 - Wasu malaman addini daga jihohin arewa su na tafa ma shugaban majalisar shugabannin coci-coci na jihohin kudu,m Martin Luther King Jr. a lokacin da yake jawabi cikin wata majami'a a Albany, Jihar Georgia a ranar 28 Agusta, 1962.

Martin Luther King Jr., yana gabatar da mashahurin jawabinsa na "Na Yi mafarki" (I Have A Dream) gaban dubun dubatan jama'a a farfajiyar ginin tunawa da shugaba Abraham Lincoln a Washington, DC, ran 28 Agusta, 1963.

Martin Luther King, Jr. rike da lambar yabo ta Nobel ta zaman lafiya wanda ya lashe a ranar 10 Disamba, 1964.

1965

1965

Gawar Martin Luther King Jr a yayin da ake kai ta makarantar Morehouse College dake Atlanta, Jihar Georgia a watan Afrilu na 1968, a bayan da wani bature ya harbe shi har lahira.