Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Hari A Adamawa Ya Halaka Mutane Biyar


Kauyen da mayakan Boko Haram suka kai hari
Kauyen da mayakan Boko Haram suka kai hari

Rahotanni daga jihar Adamawa arewa maso gabashin Najeriya na cewa mayakan Boko Haram sun sake kai wani sabon hari a yankin Madagali dake arewacin jihar, inda aka samu asarar rayuka biyar tare da jikkata wasu.

Wannan sabon hari na zuwa ne kasa da kwanaki biyu da harin da aka kai a garin Pallam dake karamar hukumar ta Madagali dake arewacin jihar Adamawa, daya daga cikin jihohin da bala'in Boko Haram ya fi shafa a Najeriya.

Shaidun gani da ido dai sun ce an kai wannan harin a kauyen Kaya dake da tazarar kilomita guda daga Gulak shedikwatar karamar hukumar Madagali. Shima da yake karin haske akan wannan hari, dan majalisar wakilai da ke wakiltar Madagali da Michika, Mista Adamu Kamale, yace al’ummar yankin na cikin zaman dar-dar a yanzu.

Lamarin da dan majalisar wakilan yace ana bukatar kai musu dauki. Kawo yanzu hukumomin tsaro a jihar Adamawan ba su yi karin haske ba tukunna, yayin da wasu al’ummar yankin suka soma tunanin sake yin wani sabon gudun hijirar.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG