Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dexter Scott King, ‘Dan Rev. Martin Luther King Jr., Ya Rasu Yana Da Shekaru 62


Dexter Scott King
Dexter Scott King

Dexter Scott King, wanda ya sadaukar da yawancin rayuwarsa kan abin da ya gada daga iyayensa Rev. Martin Luther King Jr. da Coretta Scott King na fafutukar kare hakkin dan adam, ya rasu a ranar Litinin bayan ya yi fama da cutar sankara ta prostate. Ya rasu yana da shekaru 62.

WASHINGTON, D. C. - Cibiyar King da ke Atlanta, wacce Dexter King ya yi aiki a matsayin shugabanta, ta ce ƙaramin ɗan mai fafutukar kare hakkin jama'ar ya rasu ne a gidansa da ke Malibu, jihar California. Matarsa, Leah Weber King, ta fada a cikin wata sanarwa cewa, ya rasu “salun-alun a cikin barci.”

Obit-Dexter-Scott-King
Obit-Dexter-Scott-King

Na uku daga cikin 'ya'ya hudu na Dr. King, Dexter King ya samo sunansa ne daga majami'ar Baptist ta Dexter Avenue a Montgomery, jihar Alabama, inda mahaifinsa ya yi aiki a matsayin limamin makami'ar.

Dexter King yana ‘dan shekara 7 kacal lokacin da aka kashe mahaifinsa a watan Afrilun 1968, yayin da ya ke tallafawa ma'aikatan tsaftar muhalli masu zanga-zanga a Memphis, Tennessee.

Dr. Martin Luther King Jr. da matarsa, Coretta Scott King da yaransu uku
Dr. Martin Luther King Jr. da matarsa, Coretta Scott King da yaransu uku

Dexter King ya rasu ya bar matar aure da kuma babban yayansa, Martin Luther King III; da kanwarsa, Rev. Bernice A. King; da wata matashiyar ’yar uwa mai suna Yolanda Renee King.

Coretta Scott King ta rasu ne a shekara ta 2006, sai kuma babban dan Dr. King, Yolanda Denise King, a shekarar 2007.

"Kalmomi ba za su iya bayyana bakin cikin da ke zuciyata sakamakon rasa wani ɗan'uwa na ba," in ji Bernice King a cikin wata sanarwa.

Dexter Scott King, da Rev. Bernice King, Martin Luther King III da Yolanda King
Dexter Scott King, da Rev. Bernice King, Martin Luther King III da Yolanda King

Martin Luther King na III ya ce: “Rasuwar tana da babban tashin hankali. Yana da wuya a sami kalmomin bayyana lamari irin wannan a daidai wannan lokaci. Muna rokon addu’ar ku a daidai wannan lokaci ga daukacin iyalan King”.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG