Yayin da yake magana da manema labarai, kafin Fafaroma Francis ya bar kasar Chile zuwa ta Peru, yace har sai da wata kwakkwarar shaidar da zata nuna Bishop Juan Barros na da laifi wajen kare laifuffukan lalata da ake zargin Revarand Fernando Karadima kafin ya amince da batun.
Amma idan babu wata hujja, to zai ci gaba da kallon wadannan zarge-zarge a matsayin shaci fadi. Jawabin na Fafaroman ya dagula yunkurinsa na gyara kaurin sunan da Cocin Katolika tayi na aikata masha'a da yara, kuma ya girgiza wannan jawabin ya girgiza al’ummar kasar ta Chile.
Wanda ya jawo martini daga wadanda wannan matsalar ta shafa sun yi nuni da cewar wadanda ke zargin an yarda da zarginsu matuka a Fadar Paparoman da har ta kai jallin da aka yankewa Karadima hukuncin rai da rai na “Tuba hade da yin addu’a” akan laifuuffukan daya aikata a shekarar 2011.
Facebook Forum