Za'a yiwa shanu sama da miliyan biyu da dubu dari biyar rigakafin cututtuka a kauyen Pogu da ke kusa da birnin Minna ta Jihar Neja, kamar yadda Kwamishanan kula da harkokin dabbobi da gandun daji Alhaji Haruna Nuhu Dukku ya bayyana a wajen kaddamar da wannan shirin rigakafi.
Kwamishanan kula da harkokin dabbobi da gandun dajin ya kaddamar da shirin. Yace wannan shirin ragakafin cututtuka kyauta ne a duka fadin jihar, ya kuma yi kira ga Fulani da su ja kunnuwan 'ya'yansu da su zauna lafiya da manoma.
Dr. Adamu Ibrahim Katu, likitan dabbobi a ma'aikatar da ke kula da harkokin dabbobin yayi karin haske akan allurar rigakafin. Allurar da suke yiwa shanun ta kiyaye ciwon huhunsu ce saboda ciwon yana kashe shanu da zarar sun kaamui.
Makiyayan kuma sun ce suna cikin wani halin farin ciki da allurar rigakafin. Muhammad Tukur Abubakar sarkin Fulani a wata karamar hukuma kuma shugaban Miyetti Allah 'Kaotal Hore' reshen jihar Neja yace rigakafin na da anfani saboda lokacin da aka daina yi ne cututtukan suka yawaita.
Shima mataimakin shugaban Miyetti Allah na kasa Alhaji Boso, kira yayi ga makiyaya da su ci gajiyar alherin da gwamnati ta kawo masu da tabbatar da cewa sun kai shanunsu anyi masu allurar.
Babban daraktan kula da harkokin makiyaya a ofishin gwamnan jihar Ardo Abdullahi Adamu Babaye yace, gwamnatin jihar tana daukar matakan kyautatawa makiyaya domin magance matsalolin da ake samu a bangaren Fulanin.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani
Facebook Forum