A karon farko tun bayan da gwamnatin kasar Spain ta rusa gwamnatin yankin Catalonia, majalisar dokokin zata zauna bayan zaben da ya biyo bayan matakin sakamakon yunkurin ballewar da yankin ya ayyana ta wajen kaddamar da kuri’ar raba gardama.
Jam’iyu masu ra’ayin ballewa suna da ‘yar rinjaye a sabuwar majalisar, amma wajibi ne wakilan majalisar su kafa gwamnati sannan su zabi shugabannin su.
Gabannin zaman na yau, jam’iyu biyu masu ra’ayin ballewa sun cimma jarjejeniyar zasu goyi bayan tsohon shugaban yankin Carles Puigdemont a zaman dan takara a zaben shugabannin da zasu jagoranci yankin.
Prime Ministan Spain Mariano Rajoy, yace ba za’a tsaida Puigdemont zaman dan takara ba saboda yana gudun hijira, kuma idan aka zabe shi to gwamnati zata ci gaba da aiki da dokar dakatar da diyaucin yankin.
Facebook Forum