Martanin Kasashen Duniya Kan Hambarar Da Gwamnatin Bashar Assad A Siriya

  • Murtala Sanyinna

Syria's President Bashar al-Assad answers journalists after a meeting at the Elysee

'Yan tawayen Syria sun hambarar da shugaba Bashar Assad tare da kwace iko da Damascus a ranar Lahadin da ta gabata, lamarin da ya tilasta masa yin gudun hijira tare da kawo karshen mulkin iyalansa na tsawon shekaru da dama da suka shafe sama da shekaru 13 ana yakin basasa a yankin gabas ta tsakiya.

Shugabannin kasashen duniya na ci gaba ta martani kan hambarar da gwamnatin shugaba Bashar Assad a Siriya, tare da kwace iko da Damascus babban birnin kasar, lamarin da ya tilasta masa yin gudun hijira tare da kawo karshen mulkin iyalansa na shekaru da dama.

TARAYYAR TURAI

Shugabar Hukumar Tarayyar Turai, Ursula von Der Leyen wanda ya bayyana lamarin a zaman wani babban sauyi mai cike da tarihi a yankin, ya ce Turai a shirye take ta ba da goyon baya wajen kare hadin kan kasa da sake gina kasar Siriya mai kare hakkin dukkan 'yan tsiraru."

IRAN

A cikin wata sanarwa da Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta fitar, ta ce kasar ta Iran tana mutunta hadin kan kasar Siriya da 'yancin kai na kasar, sannan ta yi kira da a gaggauta kawo karshen rikice-rikicen soji, da hana ayyukan ta'addanci, da fara tattaunawa da dukkan bangarorin al'ummar kasar ta Siriya.

Tehran ta ce, za ta ci gaba da ba da goyon bayan tsare-tsaren kasa da kasa don shata tsarin harkokin siyasa, inda ta kara da cewa, ana sa ran dangantakar abokantaka ta dogon lokaci tsakanin Iran da Siriya za ta dore.

ISRA'ILA

Shi kuwa Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu cewa yayi Rugujewar Assad, wata babbar mahada a yankin Iran, rana ce mai cike da tarihi, kuma sakamako ne kai tsaye na illar da Isra'ila ta yi wa Hizbullah da Iran.

RASHA

A cikin wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Rasha ta fitar, ta ce shugaban kasar Siriya Bashar Assad ya bar mulki tare da barin kasar bayan ya ba da umarnin a mika mulki cikin lumana.

To sai dai ma'aikatar ba ta bayyana inda Assad yake ba a halin yanzu, ta kuma ce Rasha ba ta shiga tattaunawar da ake yi na tafiyar tasa ba. Ta ce an sanya sansanonin sojin Rasha da ke Siriya cikin shirin ko ta kwana, amma babu wata babbar barazana da za ta fuskanta a halin yanzu. Moscow tana tuntubar dukkan kungiyoyin 'yan adawar Siriya tare da yin kira ga dukkan bangarorin da su guji tashin hankali.

IRAKI

A kasar Iraqi kuma, mai magana da yawun gwamnatin kasar Bassem Al-Awadi ya ce Iraki na bin diddigin abubuwan da ke faruwa tare da jaddada mahimmancin rashin tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Siriya ko kuma goyon bayan wani bangare a kan wani.

JORDAN

Shi kuwa Sarki Abdallah na Jordan ya ce kasar ta na mutunta zabin mutanen Siriya. Ya bukaci a kaucewa duk wani rikici a Siriya da ka iya haifar da rudani, tare da jaddada bukatar kare tsaron makwabciyar kasarsa ta arewa, a cewar wata sanarwa da kotun masarautar Hashemite ta fitar.

FARANSA

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce "gwamnatin dabbanci ta fadi,” yana mai yin godiya ga al'ummar Siriya, kan jajircewa da hakurinsu. Ya kuma ce a wannan lokaci na rashin tabbas, yana yi musu fatan zaman lafiya, 'yanci da hadin kai."

A cikin wani sakon da ya wallafa a shafin sada zumunta na X, Macron ya ce "Faransa za ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaron dukkan kasashen Gabas ta Tsakiya."

BURTANIYA

Firayim Ministan Burtaniya, Keir Starmer, cewa yayi "Mutanen kasar Siriya sun sha wahala a karkashin gwamnatin Bashar Assad na tsawon lokaci, kuma muna marhabin da hambarar da shi."

Ya ce "yanzu mun mai da hankali ne wajen ganin an samar da mafita a siyasance, da kuma dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali."

"Muna kira ga dukkan bangarorin da su kare fararen hula da 'yan tsiraru tare da tabbatar da cewa taimako mai mahimmanci zai iya kaiwa ga mafi rauni a cikin sa'o'i da kwanaki masu zuwa."

QATAR

Ma'aikatar harkokin wajen Qatar ta sake sabunta kiranta na kawo karshen rikicin kasar Siriya bisa ga kudurin kwamitin sulhu na MDD mai lamba 2254 na shekara ta 2015, wanda ya tanadi matakan tsagaita wuta da kuma mika mulki a siyasance. Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta ce tana bibiyar abubuwan da ke faruwa a Siriya tare da yin kira da a kiyaye hadin kan kasar.

SAUDI AREBIYA

Kasar Saudiyya cewa ta yi ta na tattaunawa da dukkan masu ruwa da tsaki a yankin kan kasar ta Siriya, kuma ta kuduri aniyar yin duk mai yiwuwa don kaucewa haifar da rudani ga kasar, kamar yadda wani jami'in Saudiyya ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

MASAR

Ma'aikatar harkokin wajen Masar ta ce Masar ta yi kira ga dukkan bangarorin Syria da su kiyaye karfin hukumomin gwamnati da na kasa. Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta tabbatar da goyon bayanta ga al'ummar Siriya da kuma 'yancin kai da hadin kan kasar.