Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar da wannan bukatar ne a daidai lokacin da take fuskantar karanfi kudi kasancewa ba a samu ko rabin kudin da aka bukata bana ba, yayinda jami’ai na fargabar manyan kasashen yammaci da suke bada gudummuwa mai tsoka da suka hada da Amurka za su zaftare gudummuwar da su ke badawa.
Sabon jami'in bada agaji na Majalisar Dinkin Duniya Tom Fletcher ya bayyana loamarin da ake fuskanta a matsayin "wahalar da ba a taba ganin irinta ba," MDD na fatan kai agaji ga mutane a kasashe 32 a shekara mai zuwa, ciki har da wadanda ke fama da yaki a Sudan, Syria, Gaza da Ukraine.
Fletcher ya shaidawa manema labarai a Geneva cewa, "Duniya na cikin TSaka Mai Wuya, kuma ta haka muka kashe wutar."
A watan da ya gabata Fletcher, tsohon jami'in diflomasiyyar Burtaniya wanda ya fara zama Shugaban Ofishin kula da ayyukan jikai (OCHA), ya ce "Muna bukatar sake daidaita dangantakarmu da wadanda ke da matukar bukata a duniya."
Duk da yake wannan shine kokon bara na hudu mafi girma a tarihin OCHA, Fletcher ya ce akwai wasu mutane miliyan 115 da hukumar ba za ta iya samun kudaden biyan bukatocinsu ba.
Ya ce, "Dole ne mu maida hankali sosai kan kaiwa ga wadanda ke cikin tsananin bukata."
Majalisar Dinkin Duniya ta zaftare tallafin kudin da ta nema na 2024 zuwa dala biliyan 46 daga dala biliyan 56 a shekarar da ta gabata, yayinda tallafin da take samu daga masu ba da gudummawa ya ragu, amma duk da haka i zuwa yanzu, an samun tallafin kashi 43% kawai, da ya kasance daya daga cikin mafiya muni a tarihi.
Amurka ta ba da sama da dala biliyan 10, kusan rabin kudaden da aka samu.
Hukumar OCHA ta ce, ma’aikatan agaji sun yi zabuka masu tsauri, da rage tallafin abinci da kashi 80% a Syria da kuma ayyukan ruwa a Yemen mai fama da kwalara.
Dandalin Mu Tattauna