Wani gagarumin yunkuri da masu ta da kayar baya suka yi a fadin kasar Syria ya kara kaimi a jiya Assabar, tare da labarin cewa sun isa kofofin babban birnin kasar, kuma dakarun gwamnati sun fice daga tsakiyar birnin Homs. An tilastawa gwamnati ta musanta jita-jitar da ake yadawa cewa shugaba Bashar Assad ya fice daga kasar.
Rasa birnin Homs wani babban koma baya ne ga Assad. Birnin na matsayin wata muhimmiyar mahada da ke tsakanin Damascus da lardunan gabar tekun Siriya na Latakia da Tartus - cibiyar da shugaban na Siriya yake da goyon baya, kuma gida ga wani sansanin sojan ruwa na Rasha.
Gidan rediyon Sham FM mai goyon bayan gwamnati ya ba da rahoton cewa, dakarun gwamnati sun mamaye wajen birnin na uku mafi girma a Syria, ba tare da yin karin haske ba.
Rami Abdurrahman wanda ke jagorantar kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil adama a Syria mai hedkwata a Birtaniya, ya ce dakarun Syria da jami’an tsaro daban-daban sun janye daga birnin, ya kara da cewa ‘yan tawaye sun shiga wasu sassa na birnin.
A karon farko a yakin basasar da aka dade ana gwabzawa a kasar, a yanzu gwamnati tana da iko ne kadai da manyan larduna uku cikin14: wato Damascus, Latakia da Tartus.
Dandalin Mu Tattauna