Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Martanin Biden, Trump Kan Hambarar Da Gwamnatin Assad A Siriya


Syrian-Americans and supporters celebrate after Syrian rebels announced that they have ousted President Bashar al-Assad in Syria, in Dearborn
Syrian-Americans and supporters celebrate after Syrian rebels announced that they have ousted President Bashar al-Assad in Syria, in Dearborn

A cikin wani jawabi da ya yi a fadar White House, Biden ya ce rugujewar mulkin dangin Assad na tsawon shekaru da dama, wata “babbar dama ce ga al'ummar Siriya don tsara makomarsu.”

Shugaban Amurka Joe Biden ya ayyana a jiya Lahadi cewa faduwar ba zato ba tsammani da gwamnatin Syria ta yi a karkashin Bashar Assad wani "babban aikin adalci ne," amma kuma ya ce "lokaci ne na rashin tabbas" ga yankin Gabas ta Tsakiya.

'Yan tawayen Syria sun hambarar da shugaba Bashar Assad tare da kwace iko da Damascus a ranar Lahadin da ta gabata, lamarin da ya tilasta masa yin gudun hijira tare da kawo karshen mulkin iyalansa na tsawon shekaru da dama da suka shafe sama da shekaru 13 ana yakin basasa a yankin gabas ta tsakiya.

Joe Biden, Shugaban Amurka
Joe Biden, Shugaban Amurka

A cikin wani jawabi da ya yi a fadar White House, Biden ya ce rugujewar mulkin dangin Assad na tsawon shekaru da dama, wata “babbar dama ce ga al'ummar Siriya don tsara makomarsu.”

Biden ya ce matakin da Amurka da kawayenta suka dauka a cikin shekaru biyu da suka gabata ya raunata masu goyon bayan Syria – wato Rasha, Iran da kuma mayakan Hizbullah da ke samun goyon bayan Iran a Lebanon - ta yadda "a karon farko," ba za su iya kare gwamnatin ta Assad ba.

Shi ma zababben shugaban Amurka Donald Trump ya fada a jiya Lahadi cewa, Assad ya arce daga kasarsa, wadda iyalansa suka kwashe shekaru da dama suna mulki, saboda na hannun damansa Vladimir Putin, shugaban kasar Rasha, “ba ya da saura sha’awar kare shi.

Donald Trump, Zababben Shugaban Amurka
Donald Trump, Zababben Shugaban Amurka

Kalaman na Trump a dandalin sa na sada zumunta sun zo ne kwana guda, bayan da ya yi Allah wadai da yiyuwar cewa Amurka na iya tsoma baki ta hanyar soji a Syria domin taimakawa ‘yan tawaye a lokacin da suke yunkurin hambarar da Assad, yana mai bayyana cewa, “WANNAN BA YAKINMU BANE”.

To sai dai mai baiwa shugaba Biden shawara kan harkokin tsaro, Jake Sullivan, ya ce gwamnatin Biden ba ta da niyyar shiga tsakani.

Amurka na da dakaru kusan 900 a Siriya, ciki har da dakarun da ke aiki tare da kawayen Kurdawa a yankin arewa maso gabashin kasar da ke hannun ‘yan adawa, domin hana sake bullowar kungiyar IS.

Dandalin Mu Tattauna

Zaben 2023

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG