Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hare-Haren Jiragen Yakin Rasha Da Na Syria A Yankin ‘Yan Tawayen Kasar Sun Hallaka Mutane 25


Wasu 'yan tawayen Syria
Wasu 'yan tawayen Syria

Akalla mutane 25 aka hallaka a yankin Arewa maso yammacin Syria sakamakon hare-haren hadin gwiwa ta sama da gwamnatin Syria da Rasha suka kai, a cewar kungiyar bada agaji ta “White Helmets” da ‘yan adawar Syria ke gudanarwa da safiyar yau Litinin.

Jiragen saman yakin Rasha da Syria sun kaiwa birnin Idlib dake yankin arewacin Syria dake karkashin ikon ‘yan tawaye hari a jiya Lahadi, a cewar majiyoyin soji, a dai dai lokacin da Shugaba Bashar Al’Asad ke shan alwashin murkushe masu tada kayar bayan da suka fantsama zuwa birnin Aleppo.

Syria-Russia
Syria-Russia

Haka kuma, rundunar sojin Syria ta yi ikirarin sake kama garuruwan da ‘yan tawayen suka mamaye a kwanakin baya-bayan nan.

Mazauna yankin sun ce daya daga cikin hare-haren ya afka cikin wata unguwa mai cunkoson jama’a a tsakiyar Idlib, birnin mafi girma a yankin ‘yan tawayen dake kusa da kan iyakar kasar da Turkiye inda kimanin mutane miliyan 4 ke zaune a tantuna da gidajen wucin gadi.

An kashe akalla mutane 7 tare da jikkata da dama, a cewar masu ceto a wurin da aka kai harin. Rundunar sojin Syria da kawarta Rasha sun ce sun kai harin ne kan maboyar masu tada kayar baya tare da musanta kai hari kan farar hula.

Yara 10 na cikin wadanda suka mutu sakamakon hare-hare ta sama kan birnin Idlib da kewaye da sauran wuraren dake karkashin ikon ‘yan tawaye a kusa da aleppo a jiya Lahadi, a cewar kungiyar bada agaji ta “White Helmets”.

Ma'aikatan White Helmets suna ceton mutane
Ma'aikatan White Helmets suna ceton mutane

Adadin mutanen da hare-haren hadin gwiwar Syria da rasha suka hallaka tun daga ranar 27 ga watan Nuwamban da ya gabata ya karu zuwa 56, ciki har da yara 20, kamar yadda kungiyar bada agajin ta wallafa a cikin wata sanarwa a shafinta na X.

Kamfanin dillancin labaran Reuters bai iya tantance bayanan daya samu daga filin daga ba.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG