Kamfanin dillancin labaran SANA ya bayyana cewa, gine-ginen na cikin yankunan Mazzeh da Qudsaya, da ke yammacin babban birnin kasar.
Gidan rediyon sojojin Isra'ila ya ce wuraren da aka kai harin a Damascus, hedkwatar kungiyar 'yan gwagwarmayar Falasdinawa ta Islamic Jihad ne da kuma abin da ta bayyana a matsayin wasu kadarori, ba tare da yin karin haske akai ba.
Isra'ila dai ta shafe shekaru tana kai hare-hare kan wuraren da ke da alaka da Iran a Syria amma ta kara kai hare-hare tun a ranar 7 ga watan Oktoban bara bayan da kungiyar Hamas ta Falasdinu ta kai hari yankin Isra'ila wanda ya haifar da yakin Gaza.
An san kwamandojin kungiyar Hezbullah ta kasar Lebanon da dakarun Revolutionary Guards na Iran da ke Syria suna zama a Mazzeh ne, a cewar mazauna yankin da suka tsere bayan hare-haren baya-bayan nan da suka yi sanadiyar mutuwar wasu daga cikin manyan kungiyoyin.
-Reuters
Dandalin Mu Tattauna