Harin dai ya faru ne akan wata hanya mai tazarar kilomita 45 kudu maso yammacin birnin Timbuktu dake arewacin Mali. Kungiyar al-Qaida ce ta fito ta dauki alhakin harin.
A wani bayani da aka fitar a yammacin jiya Alhamis jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Samantha Power, ta nuna jimamin ta ga iyalan mutane shidan da suka rasa rayukan su a dalilin harin, wanda baki ‘dayan su ‘yan kasar Burkina Faso ne.
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya ci alwashin cewa wannan harin bazai hana Majalisar Dinkin Duniya taimakawa ‘yan kasar Mali ba wajen aikin kawo zaman lafiya a kasar.
Wakilan kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya sun lura da cewa hare haren da ake kaiwa sojan kiyaye sulhu na iya zama laifukan yaki a karkashin dokar kasa da kasa.