Mutane biyar sun rasa rayukansu biyo bayan harin da wasu da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar al-Qaida ne suka kai akan sansanin sojoji dake tsakiyar kasar Mali.
Harin ya faru ne daren jiya a garin Nampala wanda yake da tazarar kilomita 530 daga babban Birnin kasar, Bamako. Garin na kan iyaka da kasar Mauritania.
Wani jami’in garin Nampala ya shaidawa Muryar Amurka sashen Faransanci cewa sojoji uku da maharan biyu suka rasa rayukansu a gwagwarmayar.
Babu wanda ya dauki alhakin kai harin nan take amma ana kautata zaton mayakan al-Qaida ne wadanda dama can suna fafitika a yankin da suka kai harin.
Idan ba’a manta ba Al-Qaida dake Maghreb da kawayenta sun taba cafke arewacin Malin a shekarar 2012 kafin sojoji a karkashin jagorancin Faransa su fatattakesu.
Daga lokaci zuwa lokaci mayakan sa kai sukan kai hari akan kafofin gwamnati da kuma sojojin kasa da kasa masu kiyaye zaman lafiya