Ma’aikatar tsaron Faransa ta fada jiya asabar cewa wata tawaga ta sojojin Najeriya da Chadi, zata shiga birnin domin tabbatar da kwanciyar hankali cikinsa. Har ila nyau, ma’aikatar ta ce magajin gari na birnin Gao, wanda ya nemi mafaka a Bamako, babban birnin kasar ta Mali, zai koma birninsa.
Wakilin Muryar Amurka Idrissa Fall, yace kama birnin na Gao yana da muhimmanci sosai a saboda ya zamo hedkwatar kungiyoyin ‘yan tawaye dabam-dabam.
Tun da fari a jiya asabar din, sojojin Faransa da na Mali, sun kwace filin jirgin saman Gao da wata gada dake kusa da nan. Ministan tsaron Faransa, Jean-Yves le Drian, yace dakarun sun yi amfani da hare-hare ta sama da kuma ta kasa domin ragargaza rumbunan kayan fada da kayan sufuri na ‘yan tawayen.
A yayin da ake ci gaba da daukar matakan sojan a cikin kasar Mali kuma, jami’an tsaro na kasashen Kungiyar Tarayyar Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAs ko CDEAO, sun gana a Abidjan a kasar Cote D’Ivoire domin tattauna yadda za a gaggauta girka sojojin yanki a Mali. Ministan tsaron Cote D’Ivoire, Paul koffi Koffi, yace jami’an ECOWAS sun kuduri aniyar tabbatar da yiwuwar hakan ba tare da bata lokaci ba, yana mai cewa, "abinda ke gabanmu yana da matukar muhimmanci a saboda ya shafi tabbatar da girka sojojin da aka yi alkawari cikin gaggawa." Yace a bayan haka, zasu nazarci bukatu na kayan aiki da yadda za a gaggauta kai su can.
Shi ma kwamandan rundunar sojojin hadin guiwar ta kasashen Afirka ta Yamma, janar Shehu Usman Abdulkadir, na Najeriya, ya halarci wannan taron, inda ya fadawa ‘yan jarida cewa aikin girka sojojin na tafiya sosai, sai dai ba zai ce ga ranar da za a kammala ba.
Har ila yau, Janar Abdulkadir yace yayi imanin ba za a samu wata matsala ba wajen hada hancin gudanar da ayyukan sojojin kasashen na Afirka, wadanda zasu fito daga kasashe masu magana da harsunan Ingilishi da Faransanci.
Kungiyar ECOWAs dai tana shirin tura sojoji dubu 3 zuwa Mali.