Shugaba Idris Deby na Chadi yace sojojinsa sun cimma gurin aikin da ya kai su can, kuma a yanzu ba zasu iya gwabza yaki salon sari-ka-noke dake kunno kai a Mali ba.
A bayan sojojin Faransa, sojoji dubu biyu na Chadi sune mafiya yawa na wata kasar waje da suka taimakawa dakarun Mali wajen kwato yankin arewacin kasar. A makon jiya, Faransa ta janye sojoji 100 a matakin farko na shirinta na janye sojojin sannu a hankali daga Mali.
A makon jiya an kashe sojojin Chadi su uku a wani harin kunar-bakin-wake a arewacin Mali, yayin da aka kashe wasu su 13 a yaki da tsagera cikin watan Fabrairu.
Ana sa ran cewa sojojin Majalisar Dinkin Duniya wadanda yawansu zai iya kaiwa dubu 11 zasu karbi ragamar ayyukan tsaro a yayin da ake kokarin maido da kwanciyar hankali tare da gudanar da sabbin zabubbuka a kasar ta Mali.
Mali ta tsunduma cikin fitina a shekarar da ta shige a lokacin da sojoji suka hambarar da gwamnati, abinda ya ba tsagera masu alaka da al-Qa’ida sukunin kwace arewacin kasar.