Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Lahadi Al'ummar Mali Za Su Zabi Gwaninsu


Soumaila Cisse (a hagu) da Ibrahim Boubacar Keita (dama) sune suka haye zuwa zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da ake yi yau lahadi a kasar Mali
Soumaila Cisse (a hagu) da Ibrahim Boubacar Keita (dama) sune suka haye zuwa zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da ake yi yau lahadi a kasar Mali

Tsohon firayim minista Ibrahim Boubacar Keita da tsohon ministan harkokin kudi, Soumaila Cisse, sune ke karawa da juna a zagaye na biyu

Yau lahadi al’ummar Mali suke zaben shugaban kasar da akasarin mutane ke fata zai jagorance ta, ya fitar da ita daga fitinar watanni 18 da ta fada a ciki.

Tsohon firayim minista Ibrahim Boubacar keita zai kara da tsohon ministan harkokin kudi Soumaila Cisse a wannan zaben fitar da gwanin da masu fashin baki da dama suke bayyana cewa zai iya zamowa harsashin sauya alkiblar kasar.

Keita shi ya lashe zagayen farko na zaben da rata mai yawa, inda ya samu kashi 40 cikin 100 na dukkan kuri’un da aka jefa, yayin da Cisse ya samu kasa da kashi 20 cikin 100. Tun bayan zagayen farko na zaben da aka yi ranar 28 ga watan Yuli, akasarin sauran ‘yan takara 25 da aka fitar sun bayyana goyon bayan ga Keita, ciki har da mutumin da ya zo na uku a zaben, Dramane Dembele.

Wannan zabe, wanda shi ne na farko da kasar zata gudanar tun 2007, ana ganinsa a zaman muhimmi wajen bude bakin aljihun kasashen ketare da suka yi alkawarin bayarda agajin dala miliyan dubu hudu ga kasar, wanda kuma aka dakatar a bayan da sojoji suka kwaci mulkin da ya jefa kasar cikin fitina.
XS
SM
MD
LG