Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Yi Taron Kasashen Duniya Kan Mali Yau Talata


Sojojin kasar Mali
Sojojin kasar Mali

Jami'an manyan cibiyoyin duniya da na gwamnatin Mali zasu yi taro yau talata a Brussels kan yadda za a tsamo kasar daga cikin matsalolinta.

Hukumomi na kasashen duniya da jami'an gwamnatin Mali zasu gana yau talata domin tattauna kokarin maido da kwanciyar hankali a kasar, a bayan da sojojin Faransa da na Mali suka kaddamar da farmakin kwato manyan biranen arewacin kasar daga hannun 'yan tawaye.

Majalisar Dinkin Duniya, da Kungiyar Tarayyar Turai, da Kungiyar Tarayyar Afirka da kuma Kungiyar Tarayyar Tattalin Arzikin AFirka ta Yamma, ECOWAS, su na kan gaba cikin kungiyoyi da hukumomi kimanin 45 da zasu shiga wannan taro na yau talata a birnin Brussels.

Za su tattauna ayyukan jinkai da na kare hakkin jama'a, da kuma harkokin siyasar kasar ta Mali, inda aka fara wannan rikici bara a lokacin da sojoji suka kifar da halaltacciyar gwamnatin shugaba Amadou Toumani Toure. Shugaban riko na kasar Mali, Dioncounda Traore, yana son gudanar da sabon zabe a watan Yuli.

Wani muhimmin batun kuma, shi ne ci gaban da aka samu wajen girka rundunar sojojin kasashen Afirka wadda zata karbi jagorancin ayyukan soja a kasar Mali daga hannun Faransawa, wadanda suka shafe makonni uku a yanzu su na jagorancin farmaki kan 'yan kishin Islama a arewacin kasar.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG