Kudurin yayi kiran da a samar da sojoji dubu 11 da 200 da ‘yan sanda 1,400 da zasu share shekara daya a wannan waje. Zasu karbi aikin tsaron wajen ran 1 ga watan Yuli daga hannayen sojojin Afirka su dubu 6. Wasu daga cikin sojojin Afrikan zasu shiga cikin dakarun zaman lafiya na MDD da zasu zauna a can Mali din.
Idan kwamitin tsaron ya amince da wannan kuduri, to fa yana da kwana 60 ya tantance idan ‘yan ta’adda na da muguwar barazana ga Mali. Kwamitin na da damar dakatar da zuba sojojin idan abubuwa a Mali suka yi tsamari.