Majalisar Dokokin Amurka Ta Amince Da Kudurin Kaucewa Rufe Ayukan Gwamnati

  • Murtala Sanyinna

'Yan majalisar dokokin Amurka suke rantsuwar kama aiki zama na 112.

An kada kuri’un amincewa 366 da suka rinjayi na kin amincewa 34, inda dan majalisa guda kuma bai da kowane ra’ayi. Dukkanin kuri'u 34 da suka nuna adawa da kudirin na 'yan jam’iyyar Republican ne.

Bayan yunƙuri har sau biyu na zartar da daftarin dokar samar da kudi ga gwamnatin Amurka, majalisar wakilan Amurka ta amince da dokar dakatar da rufewa domin samar da kuɗin tafiyar da gwamnatin tarayya har zuwa watan Maris.

An kada kuri’un amincewa 366 da suka rinjayi na kin amincewa 34, inda dan majalisa guda kuma bai da kowane ra’ayi. Dukkanin kuri'u 34 da suka nuna adawa da kudirin na 'yan jam’iyyar Republican ne.

'Yan majalisar wakilai na Republican sun cimma matsaya a tsakaninsu kan wata sabuwar bukata a jiya Juma'a. Bayan wata doguwar ganawa da 'yan majalisar na Republican, kakakin majalisar Mike Johnson ya ce sun amince da wata sabuwar shawara ta samar da kudade ga gwamnati.

Johnson ya fadawa manema labarai cewa "Akwai yarjejeniya ta bai daya da aka cimma, ita ce muna bukatar ci gaba," ya ci gaba da cewa "Amma ina tsammanin za mu ci gaba. Ba za mu bari a rufe aikin gwamnati ba.”

Yunkurin karshe na kaucewa rufe ayukan gwamnati ya zo ne bayan a ranar Alhamis ‘yan jam’iyyar Republican a majalisar, sun kasa zartar da kudirin kashe kudi wanda shugaba mai jiran gado Donald Trump ya goyi bayansa. Wannan kudiri zai kara yawan bashin da Trump ya bukata a mintunan karshe.

Da yawa daga cikin 'yan Republican sun kada kuri'ar kin amincewa da kudirin na ranar Alhamis, kuma 'yan Democrat biyu ne kacal suka goyi bayansa.

Dukan majalisun biyu - majalisar wakilai da ke rinjayen ‘yan Republican da kuma majalisar dattijai mai rinjayen ‘yan jam'iyyar Democrat - dole ne su amince da matakin domin zartar da kudurin dokar da kuma guje wa rufe gwamnati.

Shugaba Joe Biden ya fada a jiya Juma'a cewa yana goyon bayan kudirin kuma zai rattaba masa hannu.