Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ukraine Ta Kai Wa Rasha Harin Ramuwa


Russia Ukraine War
Russia Ukraine War

Jami'an Ukraine sun ce harin ya biyo ne bayan harin makami mai linzami da Rasha ta fara kai wa a Kyiv.

Kasar Ukraine ta kai hari a wani gari da ke yankin Kursk na kasar Rasha a jiya Juma'a, wanda ya kashe mutane shida ciki har da wani karamin yaro, a cewar wani babban jami’in yankin.

An kwantar da wasu mutane 10 da suka jikkata a wani asibitin da ke garin Rylsk, bayan harin da aka kai da makaman roka samfurin HIMARS da Amurka ta samar, in ji mukaddashin gwamnan Kurks, Alexander Khinshtein.

Jami'an Ukraine sun ce harin ya biyo ne bayan harin makami mai linzami da Rasha ta fara kai wa a Kyiv.

Ma’aikatar harkokin wajen Ukraine ta ce wani harin da Rasha ta kai da makami mai linzami da safiyar jiya Juma’a kan babban birnin kasar, ya kashe akalla mutum daya, ya kuma jikkata mutane 13, tare da lalata ofisoshin jakadancin kasashen waje shida da wata jami'a a tsakiyar birnin.

A shafinta na sada zumunta na telegram, rundunar sojin saman Ukraine ta ce ta kakkabo wasu makamai masu cin gajeren zango na Iskander biyar da aka harba a birnin, amma tarkacen su da suka fado sun yi barna tare da haddasa gobara a gundumomi uku. Jami'an birnin sun ba da rahoton lalacewar gine-gine da dama, da cibiyoyin kiwon lafiya da makarantu.

Jami'an rundunar sojin sama sun bukaci 'yan kasar da su gaggauta mayar da martani kan rahotannin hare-haren makami mai linzami saboda ba su ba da wadataccen lokacin neman mafaka.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG