Wata kotun Amurka ta samu wani dan Najeriya mazaunin Amurka, Oluwole Adegboruwa, mai shekaru 54, da abokin hadin bakinsa, Enrique Isong, mai shekaru 49, da laifin kitsa kafa wata muguwar kungiyar fataucin miyagun kwayoyi tare da zartar musu da daurin shekaru 40 su 2 a jumlance.
Hakan na kunshe ne a sanarwar da aka wallafa a shafin yanar gizon babban lauyan gwamnatin Amurka, na gundumar Utah a yau Juma’a.
Yayin da aka yankewa Adegboruwa hukuncin daurin shekaru 30 a gidan kaso, an kuma bada umarnin sanya idanu a kansa bayan an sake shi tsawon rayuwarsa tare da kwace fiye da dala miliyan 20 daga gare shi.
Hukuncin, da Alkalin Kotun Lardin Amurka, Jill N. Parish ya zartar, na zuwa ne bayan da mataimakan alkali suka same Adegboruwa da wanda ake tuhumarsa tare da Isong, da laifin aikata laifuffuka da dama a watan mayun 2024, ciki har da hada baki domin rarraba kwayar Oxycodone da kuma halasta kudaden haram.
A ranar 23 ga watan Oktoban 2024, aka yankewa Isong hukuncin zaman gidan kaso na shekaru 10 da kuma shekaru 3 da za’a sanya idanu a kansa bayan an sake shi.
Dandalin Mu Tattauna