Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsadar Kayayyaki Ya Sa 'Yan Najeriya Shirye-Shiryen Bukuwan Kirsimeti Cikin Kunci


Kasuwar Kayan Gwanjo
Kasuwar Kayan Gwanjo

Mabiya addinin Kirista a Najeriya za su gudanar da bukukuwan Kirsimeti na bana cikin halin kunci sakamakon matsin rayuwa da ake fama da shi a kasar.

Bikin na Kirsimeti da mabiya addinin Kirista ke yi a kowace shekara, yana zuwa ne da hada-hada da saye-sayen tufafi da sauran kayayyaki na cimaka.

To sai dai a bana wasu mabiya addinin Kirista zasu yi bikin ne dai-dai ruwa, dai-dai tsaki, saboda a cewar su, sun kaurace wa sayen sababbin tufafi sun koma sayen gwanjo, saboda tsadar rayuwa.

A hirar ta da Muryar Amurka, wata uwargida, Madam Eunice Godwin tace tsadar rayuwa ya sanya ta zuwa sayen kayan gwanjo. shima Mr Maren Zakariya yace, idan ba gwanjon suka saya ba, yaransu zasu yi Kirsimeti ne ba kaya, tunda kayan gwanjon sun fi na kanti sauki.

Kasuwar Kayan Gwanjo
Kasuwar Kayan Gwanjo

Malam Nafi'u Abdul'aziz, mai sai da kayan gwanjo a kasuwar Katako dake Jos, yace suma matsin rayuwar ya shafi harkokin kasuwancinsu, kuma suna tausaya wa kostomominsu.

Wani muhimmin sashe na bikin Kirsimeti shine yadda ake yanka kaji. Amma Kajin a bana farashinsu ya tsauwala, inda kaza daya ta kai naira dubu Ashirin, a cewar wadansu.

Shugaban kungiyar masu saida kaji a kasuwar Terminus dake Jos, Ibrahim Shehu yace, tsadar kajin ya sanya su yin taka tsan-tsan da kasuwar.

Duk da tsadar rayuwar, al’umma na fatar gwamnati zata sanya matakan samun sauki ga talaka, don shima yayi walwala.

Saurari rahoton:

Tsadar Kayayyakin Ya Sa Shirye-Shiryen Bukuwan Kirsimeti Sun Zo Wa 'Yan Najeriya Cikin Kunci
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG