Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Za Ta Karbi Alluran Rigakafin Kyandar Biri 11, 200 -GAVI


WHO Malaria Vaccine
WHO Malaria Vaccine

Wannan wani bangare ne na rukunin farko na alluran rigakafi 899, 000 da aka bayar ta hannun kawancen AAM ga kasashen Afirka 9 inda annobar tafi kamari.

A yau Juma’a Najeriya za ta karbi rukunin farko na alluran rikafin kyandar biri, 11, 200, da gwamnatin Amurka ta bada gudunmawa da taimakon kawancen “GAVI”, dake fafutuka a kan alluran rigakafi.

Sanarwar da shugaban kawancen GAVI, Dr. Sania Nishtar, ya fitar a yau tace anyi safarar alluran rigakafin zuwa Abuja, sakamakon yarjejeniyar da GAVI ya kulla ta taimakawa wajen samo gudunmawar alluran rigakafin kyandar biri 305, 000 domin agazawa kokarin duniya da nahiyar Afirka na yaki da cutar.

A ranar 24 ga watan Satumban da ya gabata, Amurka ta sanarda aniyarta ta bada gudunmawar alluran rigakafin kyandar biri da yawansu ya kai miliyan 1 domin tallafawa yaki da annobar tare da fara tattaunawa da GAVI a kan bada gudunmawar rukunin farko na allurai 305, 000.

Wannan wani bangare ne na rukunin farko na alluran rigakafi 899, 000 da aka bayar ta hannun kawancen AAM ga kasashen Afirka 9 inda annobar tafi kamari.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG