Majalisar Dinkin Duniya Ta Karfafawa Ayyukan Agaji A Morocco Da Libya

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana bakin cikinsa game da bala'in da ya afku a Libiya da Morocco.

WASHINGTON, D. C. - Da yake magana da manema labarai a ranar Laraba gabanin babban taron Majalisar Dinkin Duniya na mako mai zuwa, Sakatare Janar Guterres ya ce Majalisar Dinkin Duniya na hada kai don tallafawa ayukan agaji a kasashen biyu.

Marrakech, Morocco, 12 Sept. 2023.

Hukumomi a kasar Morocco sun sanar a ranar Laraba cewa adadin mutanen da suka mutu sakamakon girgizar kasar ya kai 2,946, yayin da wasu dubbai kuma suka jikkata.

Derna, Libya, Sept.13, 2023.

A halin da ake ciki kuma, wani rahoto na ranar Laraba na cewa adadin wadanda suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a birnin Derna da ke gabashin kasar Libya ya zarce dubu biyar, kuma ana sa ran adadin ya karu.