Adadin wadanda suka mutu sakamakon girgizar kasa mai karfin awo 6.8 da ta afku a tsaunukan Atlas da yammacin ranar Juma'a ya kai 2,862, yayin da mutane 2,562 suka jikkata, amma da alama adadin na iya karuwa.
Masu aikin ceto daga Spain, da Birtaniyya, da Qatar na taimaka wa kungiyoyin nema da ceto na Morocco, yayin da Italiya, da Belgium, da Faransa, da Jamus suka ce har yanzu ba a amince da tallafin da suka yi alkawalin bada wa ba.
Fatan samun karin wadanda suka tsira a karkashin baraguzan gine-gine na gushewa, saboda yawancin gidajen da aka fi ginawa a kauyukan dake yankin mai tsaunuka da jan bulo ake yin su, kuma sun ruguje ta yadda da wuya a tono wani abu.
Wasu da suka tsira sun kafa sansani a wani fili dauke da kunshin kayayyakinsu a kan hanyar Tizi n'Test, bayan sun tsere daga kauyukansu da bala'in ya lalata.
Wani mutum mai suna Hamid Ait Bouyali mai shekaru 40, dake jira a kai musu dauki a gefen hanya, ya ce "hukumomi suna mai da hankali kan manyan garuruwa ba yankunan karkara ba inda lamarin ya fi muni." Ya kuma ce har yanzu akwai kauyukan da ke da gawarwaki a karkashin baraguzan gine-gine.
-Reuters
Dandalin Mu Tattauna