Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sama Da Mutane 5000 Suka Rasa Rayukansu A Libya


Derna, Libya Satumba 12, 2023
Derna, Libya Satumba 12, 2023

A yau Laraba hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta kasa da kasa ta fadi cewa, mummunar ambaliyar ruwa da ta afkawa gabashin kasar Libya, ta yi sanadin raba mutane sama da 30,000 da muhallansu.

WASHINGTON, D. C. - Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane 30,000 daga cikin wadanda suka rasa matsugunansu sun fito ne daga birnin Derna, da karin dubban wasu mutanen daga wasu yankuna da suka hada da Benghazi.

Derna, Libya Sept.12, 2023.
Derna, Libya Sept.12, 2023.

Sama da mutane 5,000 ne ake kyautata zaton sun mutu, inda a yanzu yake da wuya a iya tabbatar da takamaiman adadin a kasar da bangaren gwamnatocin da ke hamayya da juna suka kwashe shekaru goma suna kokarin kama madafun iko. Wasu jami'ai sun ce adadin na iya ninkawa sau biyu.

Hichem Abu Chkiouat, Ministan kula da zirga-zirgar jiragen sama a gwamnatin da ke gabashin Libya, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa sama da gawarwaki 5,300 aka kirga a Derna ka dai. Birnin ne bala'in ya fi shafa bayan da mahaukaciyar Daniel da ta taso daga Bahar Rum ta taho da ruwan sama kamar da bakin kwarya, lamarin da ya haddasa ballewar madatsun ruwa guda biyu.

Ambaliyar ruwa a Libya
Ambaliyar ruwa a Libya

Fatma Balha, wata daliba a fannin aikin likita a Derna, ta shaidawa Muryar Amurka cewa an samu barna sosai a tsakiyar birnin Derna.

“Babu komai yanzu. Duk gine-ginen sun rushe. Duk ruwa ya tafi da su, watakila ruwan ya ja su zuwa teku. Bamu iya ganin ginin, ” in ji Balha. “Akwai 'yar uwar mahaifiyata, tana can, ba mu iya gano ta ba da 'ya'yanta, babu kuma gawarwakinsu. Ko ginin ba a gani ba. Ya tafi.”

‘Yan kungiyar Red Crescent suna bada taimako a Libya
‘Yan kungiyar Red Crescent suna bada taimako a Libya

Kungiyar agajin kasa da kasa ta Red Cross da Red Crescent, a yau Laraba ta ce lamarin a birnin Derna ya yi muni matuka, kuma ana bukatar tallafin kasashen waje.

Mey Al Sayegh, shugaban sadarwa na ofishin IFRC na Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka, ya fada a cikin wani takaitaccen bayani kan Twitter cewa babu tsaftataccen ruwan sha a Derna, babu magunguna, kuma asibiti daya tilo a birnin ba zai iya ci gaba da karbar marasa lafiya ba.

Al Sayegh ya ce abin da ake bukata a yanzu shi ne ruwa, matsuguni, agajin magani, abinci da kuma tallafin zamantakewa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG