Mahaukaciyar guguwar Daniel da ta taso daga Bahar Rum a daren Lahadin da ta gabata ta haifar da barna da ambaliyaR ruwa a garuruwa da dama da ke gabashin Libya amma birnin Derna lamarin ya fi shafa, inda ruwan sama kamar da bakin kwarya da kuma ambaliya suka sa madatsun ruwa ballewa tare da shafar daukacin unguwanni.
Othman Abduljaleel, Ministan lafiya na gwamnatin gabashin Libya ya ce "Al'amarin yana da matukar muni." Har yanzu akwai gawarwaki kwance a kasa a sassa da dama na birnin. Asibitoci sun cika da gawarwaki, kuma akwai wuraren da har yanzu ba a samu damar isa don kai agaji ba," a cewar Abduljaleel.
Hukumar motocin daukar marasa lafiya da agajin gaggawa da ke shirya ayyukan bincike da ceto, ta fada yau Talata cewa kimanin mutane 2,300 ne suka mutu a Derna kadai, ba tare da bada karin bayani ba.
Masu bayar da agajin gaggawa da suka hada da sojoji, da ma’aikatan gwamnati, da masu aikin sa kai, da kuma mazauna wurin sun yi ta tona baraguzan gine-gine a kokarin gano gawarwaki. Sun kuma yi amfani da kwale-kwale don kwashe gawarwakin daga cikin ruwan.
Har yanzu dai masu aikin hako abubuwa da sauran kayan aiki ba su isa garin Derna ba.
-AP
Dandalin Mu Tattauna