Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mummunar Guguwar Tekun Baharum Ta Kashe Akalla Mutane 25 A Gabashin Libiya


Wata guguwa mai tsanani a Tekun Baharum ta sauka a gabashin Libya a ranakun Lahadi da Litinin, inda ta kashe mutane akalla 25 tare da lalata gidaje da hanyoyi, in ji majiyoyin lafiya.

WASHINGTON, D. C. - Kakakin LNA Ahmad Mesmari ya ce wasu sojoji bakwai daga cikin sojojin kasar Libya sun bace.

Hotunan da aka yada a shafukan sada zumunta sun nuna yadda mutane suka hau kan rufin motocinsu yayin da suke kokarin neman a ceto su daga ambaliyar ruwa da guguwar Daniel ta haifar da ta afkawa garuruwan Benghazi, Sousse, Al Bayda, Al-Marj da Derna.

Wani mazaunin Derna Ahmed Mohamed ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ta wayar tarho ranar Litinin cewa, "Muna cikin barci, amma lokacin da muka tashi, sai muka tarar da ruwa ya mamaye gidan, muna ciki muna kokarin fita,".

Shaidu sun ce ana ci gaba da gudanar da bincike da kokarin ceto. Hukumomi sun ayyana dokar ta baci, tare da rufe makarantu da shaguna da kuma sanya dokar hana fita.

Wasu manyan tashoshin mai guda hudu a Libya, Ras Lanuf, Zueitina, Brega da Es Sidra, sun kasance duka a rufe daga yammacin ranar Asabar na tsawon kwanaki uku, kamar yadda injiniyoyi biyu suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Firai Ministan Gwamnatin rikon kwarya a Tripoli, Abdulhamid Dbeiba, ya ce a ranar Lahadin da ta gabata, ya umarci dukkanin hukumomin kasar da su “yi gaggawar magance barna da ambaliyar ruwa ta janyo a garuruwan gabashin kasar.

Majalisar Dinkin Duniya a Libya ta ce tana bin sahun yawon guguwar sosai kuma za ta ba da agajin gaggawa don bada tallafi ga kananan hukumomi da na kasa baki daya.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG