Majalisar Dinkin Duniya ta ce Sudan ce ta kai harin bam ran Alhamis daura da wani sansanin ‘yan gudun hijiran da ke Sudan ta Kudu.
Shugaban rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya Herve Ladsous ya fadi jiya Jumma’a cewa tabbacin cewa Sudan ce ta kai harin ya fito ne daga ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Sudan ta Kudu.
Ladsous y ace dakarun Sudan sun jefa bama bamai akalla 2 daura da sansanin ‘yan gudun hijira na Yida, wanda ke dauke da kimanin mutane 10,000 da suka rasa muhallansu sanadiyyar yakin da ake yi a ketare a Kudancin Kordofan na Sudan.
Wani jami’in gwamnati da ke wurin y ace an hallaka a kalla muatne 12 a harin, to amman Ladsous y ace har yanzu ba a san adadin wadanda abin ya rutsa da sub a.
Wannan harin ya jawo suka daga Amurka da cibiyar Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da ‘yan gudun hijira. Jiya Jumma’a Kwamishinan Hakkin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya Navi Pillay yay i kiran da a gudanar da bincike game da harin.
A gefe daya kuma Jakadan Sudan a Majalisar Dinkin Duniya Daffa-Alla Elhaq Ali Osman ya gaya wa manema labarai bayan taron da kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya yay i game da batun cewa rahotannin na kage ne; babu wani harin bam a sansanin ‘yan gudun hijiran.