Majalisar Dinkin Duniya tace rikicin Somalia tana matukar illa ga yaran kasar.
Asusun kula da yara ta Majalisar (UNICEF), yace an kashe yara 24 wasu 58 suka jikka a kasar cikin watan Okotoba,wan nan adadin shine mafi yawa a duk shekaran nan.
A cikin sanarwa da asusun ya bayar yau talata, yace galibin yaran ana rutsawa dasu a fadace fadace da ake yi. Baki daya asusun yace an kashe yara fiyeda dari cikin wan nan shekara.
Haka kuma Asusun yace fiyeda yaran Somalia 600 ne aka tilastawa shiga aikin soja, yayinda mata metan galibinsu ‘yan mata aka yi wa fyade.
Asusun UNICEF yana kira ga duka sassa a rikicin na Somalia su daina kisa da nakasawa da fayde da suke yi wa yara.