Hankali na kara tashi a Liberia yayinda ‘yan takarar shugaban kasar dake hamayya da juna ke tsirawa juna hannu bisa zargin yiwa masu kada kuri’a barazana ana saura kwanaki a gudanar da zaben fidda gwani.
Tsohon ministan shari’a Winston Tubman ya yi kira ga mutanen kasar Liberiya su kauracewa zaben da za a gudanar ranar Talata inda yake kalubalantar shugaba Ellen Johnson Sirleaf. Yana zargin cewa, irin rashin gaskiyar dake hukumar zabe ya sa ba za a gudanar da sahihin zabe ba.
A cikin jawabin da tayi ga kasa, shugaba Sirleaf ta zargi Tubman da keta kundin tsarin mulkin kasa tare da zuga al’ummar kasar Liberia su yi watsi da ‘yancinsu na kada kuri’a. Shugabar kasar tace Tubman yana so ya janye daga takarar ne sabili da yasan zai fadi zabe.
Amurka ta bayyana takaici jiya asabar cewa Tubman yana kira da a kauracewa zaben bisa ga cewar Amurka ba a iya tabbatar da zargin magudi a zaben da aka gudanar ranar 11 ga watan Oktoba ba.
Shugaba Sirleaf ta sami sama da kashi 40% na kuri’un a zagayen farko na zaben. Tubman wanda ya sami sama da kashi 30% yana zargin cewa an tafka magudi domin jami’an zabe sun sake adadin kuri’un zaben.
Masu sa ido daga cibiyar Carter da kuma kungiyar hadin kan tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika sun ce matsalolin da aka samu a zagayen farko na zaben basu taka kara sun karya ba