Wata ‘yarmajalisar dokokin Ghana tace majalisarsu tayi harramar daukar matsayi dangane da batun kafa dokokin zasu haramta liwadi da madigo a kasar. A ranar Larabar shekaranjiya ne shugaban Ghana din, John Atta Mills yace shi har abada, ba zai taba goyon bayan duk wani yunkurin halitta wannan dabi’ar a Ghana ba. Shugaban yana maida murtani ne ga barazanar da Prime-ministan Ingila David Cameron yayi na cewa Ingila zata tsinke agajin da take baiwa duk wata kasar da ke da dokokin da suka haramta liwadi da madigo. ‘Yar majalisar dokoki Malama Catherine Afeku ta gaya wa VOA cewa aksarin dukkan ‘yanmajalisar tasu na goyon bayan a kafa dokokin don a san matsayin da za’a dauka kan zancen liwadi da madigo, musamman da yake dokokin da ake da su yanzu a Ghana basu haramta wannan dabi’un ba.
Ghana na shirin kafa dokokin haramta liwadi da madigo a kasarta