Kungiyoyin rajin kare hakkin bil'adama sun sa ayar tambaya kan sahihancin zaben raba gardamar da aka yi a Equitorail Guinea ranar Lahadi, wanda jami’an gwamnati suka ce ya kusa kai ga amincewa da shirin yin garanbawul ga kundin tsarin mulkin kasar da gagarimin rinjaye.
Kungiyar Human Right Watch mai hedikwata a birnin New York da kuma kungiyar Equatorial Guinea EQ Justice sun ce sun ga inda aka sa mutane kada kuri’a a bayyane yayinda kuma wadansu ke kada kuri’a a madadin ‘yan uwansu. Sun kuma ga sojoji a wadansu tasoshin zabe da kewayen wuraren. Su ka kuma ce an yi ta barazana ga ‘yan adawa aka kuma kama mutane biyu.
Jami’an gwamnatin suka ce sakamakon wuccin gadi ya nuna kashi 99% sun zabe amincewa ne da garanbawul din, wanda ya hada da sabon wa’adi ga shugaban kasa da kuma kirkiro da mukamin mataimakin shugaban kasa.
Masu sukan sabon kudin tsarin mulkin kasan sun ce zai kara iko ga shugaba Teodoro Obiang Nguema ne ya kuma bashi damar yin gaban kanshi wajen zaban wanda zai gaje shi.