Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sudan Ta Kori Jakadan Kenya


Shugaba Omar Hassan al-Bashir na Sudan yana jawabi a Khartoum a watan Fabrairun 2011
Shugaba Omar Hassan al-Bashir na Sudan yana jawabi a Khartoum a watan Fabrairun 2011

A bayan da babbar kotun Kenya ta umurci gwamnati da ta kama shugaba Omar al-Bashir na Sudan idan ya taka kasar Kenya.

Sudan ta kori jakadan Kenya dake kasarta, a bayan da Babbar Kotun Kenya ta bayarda takardar iznin kama shugaba Omar al-Bashir na Sudan idan ya taka kafa cikin Kenya.

Jiya litinin kotun ta Kenya ta bayarda umurni ga gwamnatin kasar da ta kama shugaba al-Bashir idan ya sa kafarsa a Kenya. Kotun bin kadin manyan laifuffuka ta duniya tana neman shugaba Bashir bisa zargin ya aikata laifuffukan yaki da kisan kare-dangi a yankin Darfur na Sudan.

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun soki lamirin kasar Kenya saboda ta ki kama shugaba Bashir a lokacin da ya halarci bukukuwan murna da sabon tsarin mulkin Kenya a cikin watan Agustan 2010 a birnin Nairobi.

Wani kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sudan ya fada jiya litinin cewa gwamnati a birnin Khartoum ta umurci jakadan Kenya da ya bar kasar cikin sa’o’i 72, watau kwanaki 3. Har ila yau yace Sudan ta kuma umurci jakadanta dake Kenya da ya komo gida.

Sudan dai ba ta amince da ikon kotun bin kadin manyan laifuffuka ta duniya ba, kuma shugaba al-Bashir yayi ko oho da wannan takardar sammaci da kotun ta bayar ta hanyar yin tafiye-tafiye a kasashen waje sau da dama.

Aika Sharhinka

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG