Hakan na zuwa ne bayan da Shugaban Kasa Bola Tinubu ya aikewa Majalisar Dattawan wasika a jiya Talata, ya na bukatar a tabbatar da Kekere-Ekun a matsayin Babbar Jojin Najeriya.
Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, ne ya karanta wasikar a zauren majalisar a jiya Talata.
Shugaban kasar ya bayyana kwarin gwiwarsa game da zabenta da aka yi sannan ya bukaci majalisar ta gaggauta daukar mataki akai.
A Agustan da ya gabata, Majalisar Harkokin Shari’a ta kasa (njc) ta baiwa Shugaba Tinubu shawarar nada Mai Shari’a Kekere-Ekun a matsayin wacce zata gaji tsohon babban jojin Najeriya, Mai Shari’a Olukayode Ariwoola.
Kekere-Ekun ce babbar jojin Najeriya ta 23 kuma mace ta 2 da ta taba hauwa wannan mukami.
Mace ta farko da ta hau kan wannan mataki ita ce Mai Shari’a Maryan Aloma Mukhtar, wacce ta rike mukamain alkalin alkalan Najeriya tsakanin watan Yulin 2012 da Nuwambar 2014.