Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawan Najeriya Ta Tabbatar Mambobin Kwamitin Manufofin Kudi Na CBN


Banban Bankin Najeriya CBN
Banban Bankin Najeriya CBN

Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin mutane 12 a matsayin mambobin Kwamitin kula da Manufofin Kudi na Babban Bankin Najeriya (CBN).

Tabbatarwar na zuwa ne bayan kammala nazarin rahoton kwamitin akan harkokin banki da inshora da kuma sauran cibiyoyin hada-hadar kudi a yayin babban taronsa daya gudana a yau alhamis.

Tabbatar da sabbin mambobin kwamitin na zuwa ne ‘yan kwanaki kafin fara taron farko na babban bankin akan manufofi karkashin sabon gwamnan bankin na cbn. an dai tasara gudanar da taron tsakanin ranaikun 26 da 27 ga watan febrairun da muke ciki.

Mambobin kwamitin sun hadar da:

1. Olayemi Cardoso – Shugaba

2. Muhammad Sani Abdullahi – Mamba

3. Bala M. Bello – Mamba

4. Emem Usoro – Mamba

5. Philip Ikeazor – Mamba

6. Lamido Yuguda —Mamba

7. Jafiya Lydia Shehu – Mamba

8. Murtala Sabo Sagagi – Mamba

9. Aloysius Uche Ordu – Mamba

10. Aku Pauline Odinkemelu – Mamba

11. Mustapha Akinwumi –Mamba

12. Bandele A.G. Amoo –Mamba

A watan Wuwambar daya gabata, Cardoso, wanda ya kasance sabon gwamnan babban bankin Najeriya da Shugaban Kasa Bola Tinubu ya nada a watan Satumbar shekarar data gabata, yace kwamitin manufofin kudi bai yi aiki yadda ya dace ba karkashin mutumin daya gada akan mukamin, Godwin Emefiele.

“Tsawon lokaci, taron kwamiitin manufofin kudin baya aiki yadda ya dace”, “ a cewarsa, inda ya kara da cewar “dokar gudanar da bankin na CBN ta shekarar 2007 ta bukaci a rika gudanar da taron kwamitin sau 4 a shekara kuma bankin ya cika wannan ka’ida a shekarar 2023.

Ya nanata cewar ''za mu maida hankali akan tabbatar da cewar irin wadannan tarurruka sun yi tasiri tare da aiki yadda ya dace.”

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG