Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya nada Farfesa Abdullahi Saleh Usman a matsayin sabon shugaban hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON.
Nada Farfesa Usman ya biyo bayan sauke Jalal Arabi, wanda ya shugaban ya nada a bara.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC na tuhumar Arabi kan yadda aka sarrafa naira biliyan 90 da gwamnatin tarayya ta bayar don tallafa wa aikin hajjin 2024.
Ana zargin Arabi da wasu jami'an hukumar da karkata akalar wani adadi na wadannan kudade.
Wata sanarwa da kakakin Tinubu Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Litinin ta ce Farfesa Usman fitaccen malami ne da ya yi karatu a Jami’ar Madinah da Jami’ar Pashewar da ke Pakistan.
“Sannan ya san kan aikin hajji duba da cewa ya taba rike hukumar alhazai ta jihar Kano wacce ta fi yawan alhazai a duk fadin kasar.
“Nadin zai tabbata idan majalisar dattawa ta sahale.” In ji Ngelale.
Dandalin Mu Tattauna