Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar Almajirai


Shugaban Najeriya Ahmed Asiwaju Tinubu
Shugaban Najeriya Ahmed Asiwaju Tinubu

Shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu ya amince da nadin sabon shugaban hukumar Almajirai da ilimin yara wadanda ba sa zuwa makaranta.

Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada Ja’afaru Isa, shugaban hukumar kula da Almajirai da ilimin yaran da ba su zuwa makaranta yayin da Dr Idris Sani zai zama Babban Sakatare, kamar yadda da Cif Ajuri Ngelale, mashawarcin shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja.

Ja'afaru isa
Ja'afaru isa

Ya ce Ja’afar-Isa shugaba ne da ake girmamawa kuma a baya ya yi aiki a matsayin tsohon gwamnan Kaduna daga 1993- 1996.

Shugaban ya kuma amince da nadin Tijjani Abbas a matsayin babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin masarautu.

“Shugaban kasa yana sa ran sabbin wadanda aka nada za su yi amfani da kwarewar da suke da ita wajen gudanar da wannan muhimmin kwamiti, wanda ke tasiri a cikin al’umma.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG